Translator from Hausa to English: Richard Akindele.
[b]Bayanin Naira[/b]
The meaning of Naira,
[b]Daidai na bayanin naira.[/b]
Exact meaning of Naira.
[b]Bayanin Naira.[/b]
The meaning of naira.
[b]Bayanin Naira, yanzu shi nake son baku.[/b]
The meaning of naira is what I'm about to give you.
[b]Naira dai namu abu mai maganin sirkan zamani.[/b]
Naira, the medicine of modern ailments.
[b]Naira dai namu abu mai maganin matan zamani.[/b]
This our naira, is the medicine of modern women.
[b]Yanzu zamanin nan namu, [/b]
In this modern age,
[b]mai kudi shi ke da mutunchi.[/b]
only the rich has any dignity.
[b]In ka na da naira,[/b]
If you've got naira,
[b]ko karya ka fada, ta zauna.[/b]
Any lie you tell, stands as truth.
[b]Amma in baka da naira,[/b]
But if you've got no naira,
[b]Mahaukachin kare ya fi ka.[/b]
Even a mad dog is better than you.
[b]Yanzu zamanin nan namu,[/b]
In this modern age of ours,
[b]kun ga Dan Azumi Baba,[/b]
you see elder Dan Azumi Baba,
[b]domin bashi da naira, [/b]
because he has no naira,
[b]in ya yi magana,[/b]
when he talks,
[b]Mutane sai a che da shi yayi karya,[/b]
people will call him a big liar,
[b]koko a che dashi dan moula ne.[/b]
or he would be called crazy.
[b]Ko a che masa ya sha daga,[/b]
or accuse him of being on drugs.
[b]Amma in kana da naira,[/b]
However, if you've got naira,
[b]sai ka karkache hular ka[/b]
you would slant your cap
[b]kamar da Rarrafe Kuyituba, sai ya karkache hular sa.[/b]
like Rarrafe Kuyituba slants his hat.
[b]Ya dinga zuba muku karya.[/b]
And be lying to everybody through his teeth.
[b]Saboda a kwai kudi a gurin sa,[/b]
Because he's loaded financially,
[b]duk jama'a ta gurin suna dadai ne,[/b]
everybody around would be agreeing with all he says,
[b]wannan magana daidai ne.[/b]
every thing you're saying is absolutely correct.
[b]Ai ko mun gani a hadis.[/b]
Infact, we've seen it in hadis.
[b]Mutan zamani.[/b]
The Modern individual,
[b]idan sun ganka da naira,[/b]
once they see you with naira,
[b]in kayi magana a mutane,[/b]
if you speak to people,
[b]sai ka ji sun yi jawabi,[/b]
you'd see them deliberating among themselves,
[b]sai su che shi dama, Alhaji ai mun san shi,[/b]
they would be saying we know Alhaji well.
[b]tun yana karami, Alhaji bai taba yin karya ba.[/b]
right from childhood, Alhaji has never told a lie.
[b]Amma in baka da naira,[/b]
But if you have no naira,
[b]komai ka fada, karya che.[/b]
Whatever you say is a lie.
[b]Yanzu zamani ya changa.[/b]
Times have changed now.
[b]Su ma matan zamani, sai da kudin ka suke kaunarka[/b]
Even modern day women, only when you have money do they love you.
[b]Mache duk kaunar da take ma, ka yi kokari ka nemo naka.[/b]
Regardless of a woman's love toward you, work hard to bring home money.
[b]Ka yi kokari ka nemo naira.[/b]
Struggle to find naira.
[b]Idan ta ganka da naira, sai ka gani kauna ta mike.[/b]
When she sees you with naira, suddenly you'd see love blossom.
[b]Idan kuwa baka da naira, sai ka gani kauan ta kare.[/b]
But if you have no naira, suddenly you'd see love vanish.
[b]Nima da ka ganmi makaho,[/b]
Even me a blindman,
[b]matan zamani, na riga na gane halin su.[/b]
modern woman, I've already understood their behavior.
[b]kaman Fati Bararode, ko Maryam Bubar Aliyu.[/b]
Just like Fati Bararode, or Maryam Bubar Aliya.
[b]in suka gan ni da dubban naira.[/b]
if they see me with a boat load of naira.
[b]ku duba kyawun Maryam Omert, koko Fati Bararode.[/b]
See how beautiful Maryam Omert is, or Fati Bararode.
[b]Kunga dai makaho ne ni, in nache inna kaunar su,[/b]
As you can see I'm a blindman, if I say I like them,
[b]saboda dubban naira, sai su durkusa a gaba na.[/b]
because of my loads of naira, they would kneel before me.
[b]Sai su che to mallam, ai mutum ba zai ki mutum ba[/b]
They would say, hey Mr. a human cannot reject another human.
[b]Tun da kana kaunar ta, ni ma ina kaunar ka,[/b]
Since you like me, I too like you,
[b]Shi aure babu haramu.[/b]
Marriage is not forbidden.
[b]Har me ka ji tayi wa'azin ta,[/b]
You would even hear her preaching,
[b]sai ta che mallam, ai Allah ne ya yi ka,[/b]
you would hear her say, it's God that made you,
[b]kuma ni ma Allah ya yi ni.[/b]
same as God made me too.
[b]Ni da kai, ai ba banbanchi.[/b]
You and I, there is no difference.
[b]I dan nache yarinya, kin san babu ido a gare ne,[/b]
If I say lady, you know I have no eyes,
[b]Sai ta che, kai mallam manta da makanta.[/b]
She would say, hey Mr, please forget that nonesense.
[b]Manta da makanta, masu idon ma, me suka fi ka.[/b]
Forget that nonesense, even those with eyes how are they better than you.
[b]Ga ka dan tsirin yaro, kuma ga kyaun fuska.[/b]
You slender boy, plus handsome face.
[b]Kuma ga ka da dubban naira.[/b]
Then there you are with loads of naira.
[b]Don Allah manta da makanta.[/b]
For God's sakes forget the nonesense.
[b]Maryam Umar an ganni da naira.[/b]
Maryam Umar sees me with naira.
[b]Amma in bani da naira,[/b]
But if I don't have naira,
[b]Ko da mummuna che,[/b]
Even if she's ugly,
[b]In na che ina kaunar ta,[/b]
If I say I like her,
[b]Sai ta koma gefe ta che, laila ilallahu,[/b]
She would run to a corner, and say oh my goodness gracious!
[b]Yanzu ka dubi kama ta, ka che niche matar ka.[/b]
Now for you to see somebody like me, and say you want me.
[b]Ko babu maza a garin nan,[/b]
Even if there are no men in this town
[b]Ni me zan yi da makaho,[/b]
What would I do with a blindman,
[b]Yaya zanyi na auri makaho,[/b]
How in the world would I marry a blindman!
[b]Ai ko matarka ta aure,[/b]
Even your matrimonial wife,
[b]ai sai da kudin ka take kaunarka.[/b]
only when you have money would she love you.
[b]In ta gan ka da naira,[/b]
When she sees you with naira,
[b]in ta gan ka da naira, ranna sai ga ji sabon suna,[/b]
when she see you with naira, that day you would hear a near name
[b]sai ka ji ta kira Honi,[/b]
you would hear her call you honey,
[b]ko kuwa tache maka da Dalin[/b]
or she would call you Darling.
Ai nan baka san komai ba,
You haven't heard anything yet,
[b]ai ma ta kira ka da Sharifi,[/b]
she would even call you Sheriff,
[b]in ka gane zugar ta, ka kone.[/b]
when you understand her buttering you up, you would melt.
[b]Wai matar ka ta aure,[/b]
Your own matrimonial wife,
[b]Idan ta ganka da naira,[/b]
When she sees you with naira,
[b]Sai ta che Haji baitin lahi.[/b]
She would say Alhaji your highness.
[b]Idan kuma baka da naira,[/b]
But then if you have no naira,
[b]sai ta kira ka da gautan ladi.[/b]
she would call you with disgust.
[b]A kudin mu ta naira,[/b]
In our currency naira,
[b]dubu guda ita che Asamahu.[/b]
is Sabara'u.
[b]Ka san sabara'u, maisa ka mai da arne mallam.[/b]
You know sabara'u makes you turn a devil into a gentleman.
[b]Idan ka ganshi da naira,[/b]
when you see him with naira,
[b]sai ka durkusa a gaban sa,[/b]
you would kneel before him,
[b]ka dinga che masa...[/b]
you would be saying...